Hukumar Ilimin Bai Daya Ta Jiha Ta Shirya Taron Bita Ga Jami’an Kula da Dakunan Karatu 220
Hukumar Ilimin Bai Daya Ta Jiha Ta Shirya Taron Bita Ga Jami’an Kula da Dakunan Karatu 220

Daga Usman Da’u Isah/JB Danlami
Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano ta shirya wani taron bita na musamman ga jami’an kula da dakunan karatu 220 da ke makarantun firamare da kananan makarantun sakandare a fadin jihar.
Ana gudanar da taron ne a cibiyar bayar da horo ta hukumar da ke Kwalejin Sada’atu Rimi, Kumbotso.
Taron na tsawon yini biyu, ya kunshi jami’an da aka zabo daga kananan hukumomi 44 na jihar, tare da nufin koya musu sabbin dabarun lura da dakunan karatu domin inganta amfaninsu a makarantu.
Da yake jawabi wajen bude taron, shugaban hukumar Ilimin Bai Daya na jiha Malam Yusuf Kabir wanda Daraktar sashen horas da malamai, Hajiya Hauwa Tanimu, ta wakilta, ya bayyana muhimmancin dakunan karatu a matsayin muhimmiyar cibiyar ilmantarwa.
Ya ce dakunan karatu na taimaka wa dalibai da malamai wajen samun karin ilimi, bincike da habaka basira.
Malam Yusuf Kabir ya bayyana cewa, samun dakunan karatu masu inganci a makarantu yana karfafa sha’awar karatu ga ɗalibai, tare da bai wa malamai damar samun sabbin kayan karatu da dabarun koyarwa na zamani.
Ya ci gaba da cewa wannan taro na daga cikin matakan da hukumar ke dauka bisa sahalewar Gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, domin inganta harkar ilimi a jihar.
Shugaban ya kuma ja hankalin mahalarta taron da su mayar da hankali kan abubuwan da za’a koya musu, tare da bukatar shugabannin makarantu da malamai su rungumi amfani da dakunan karatu da kuma fadakar da ɗalibai kan muhimmancinsu domin haɓaka ilimi a makarantu.
Shugaban hukumar kula da dakunan karatu ta jiha, Alhaji Kabiru Ado Zakirai, ya bayyana taron a matsayin wata kafa ta ilmantarwa, inda za a gabatar da jawabai daga masana, nuna sabbin kayan aiki da ake amfani da su a dakunan karatu, da kuma tattauna hanyoyin da za a inganta ayyukan dakunan karatu a makarantu.
A nata jawabin, mai taimakawa gwamna ta musamman kan harkokin dakunan karatu, Hajiya Hauwa Halilu, ta yaba da irin matakan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke dauka wajen inganta ilimi a jihar.
Babban jami’in cibiyar YUSUFA kuma jagoran bayar da horon, Dr. Yakubu Anas, ya bayyana taron a matsayin hadin gwiwa tsakanin Hukumar Ilimin Bai Daya ta jiha, hukumar kula da dakunan karatu ta jiha, da cibiyar bunkasa ilimi ta YUSUFA.
Wasu daga cikin mahalarta taron, Malam Ibrahim Imam da Malama Rabi Tijjani, sun nuna godiya ga shugaban hukumar Ilimin Bai Daya, Malam Yusuf Kabir, bisa irin kokarinsa na kawo sauye-sauye masu inganci a fannin ilimi. Sun kuma sha alwashin amfani da damar bitar don samun karin kwarewa a aikinsu na kula da dakunan karatu.


