Labarai

NASU SUBEB ta taya Gwamna Abba Kabir Yusif Murnar Karramawa Daga Jaridun Vanguard da Leadership

NASU SUBEB ta taya Gwamna Abba Kabir Yusif Murnar Karramawa Daga Jaridun Vanguard da Leadership

Daga JB Danlami

Kungiyar ma’aikata wadanda ba malamai ba, reshen Hukumar Ilimin Bai Daya (NASU SUBEB), ta nuna farin cikinta tare da sauran al’umma wajen taya Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, murnar samun lambar yabo daga jaridun Vanguard da Leadership.

Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwar taya murna da ke dauke da sa hannun Shugaban kungiyar reshen Hukumar Ilimin Bai Daya, Kwamared Aminu Ali Mai Kudi

A cewar Kwamared Aminu, wanna karramawa ta zo a kan gaba, kuma ya dace a yaba wa Gwamna Abba bisa namijin kokarinsa na inganta rayuwar al’umma, musamman a bangaren ilimi.

“‘Ya’yan kungiyar sun ci gajiyar tsare-tsaren Gwamnati wajen inganta walwalar ma’aikata, ciki har da aiwatar da karin girma da kuma sanya mafi karancin albashi,” in ji Kwamared Aminu.

Shugaban kungiyar ya jaddada cewa NASU SUBEB za ta ci gaba da mara wa tsare-tsaren Gwamnatin Jihar Kano baya, musamman wadanda suka shafi bunkasa ilimi da jin dadin ma’aikata.

Haka zalika, ya bayyana cewa kungiyar za ta sanar da uwar kungiyar ta jiha da ta kasa irin ayyukan alherin da Gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusif ke aiwatarwa a fannin ilimi, domin kar su tsaya kawai a gani ba tare da yaba masa ba.

“Za mu tabbatar da cewa muryar alheri ta kai ga uwar kungiyar ta kasa da kuma jiha, domin su fahimci irin jajircewar Gwamnan mu wajen kawo sauyi a bangaren ilimi,” in ji shi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button