Labarai

Shugaban AoPSHON Na Kano ya yabawa Gwamna Abba Kan Karramawar Ayyukan Raya Kasa

Shugaban AoPSHON Na Kano ya yabawa Gwamna Abba Kan Karramawar Ayyukan Raya Kasa

Daga JB Danlami

Shugaban Kungiyar Shugabanin Makarantun Firamare na Jiha (AoPSHON), Kwamared Malam Abdussalam, ya bayyana cewa karramawar da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke samu daga bangarori daban-daban alama ce ta amincewa da kokarin da Gwamnatinsa ke yi wajen raya jiha.

Malam Abdussalam ya bayyana hakan ne yayin da yake karin haske kan lambar yabo da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu daga manyan jaridu guda biyu, Vanguard da Leadership. Wadannan jaridu sun karrama shi a matsayin Gwamnan da ya fi kowa fice wajen ayyukan raya kasa a shekarar 2024.

Sanarwar ta fito ne ta bakin Sakatariyar kungiyar ta jihar Kano, Kwamared Bilkisu Abdulkadir.

A cewar shugaban AoPSHON, kungiyar na cikin sahun gaba wajen yabawa Gwamna Abba Kabir bisa tsare-tsaren inganta harkar ilimi da ya fito da su. Ya ce Gwamnatin ta inganta walwalar malamai ta hanyar samar da kayan aiki, kujerun zaman dalibai da na malamai a makarantun firamare

“Muna godiya matuka bisa yadda Gwamnatin ta yi mana karin albashi da kuma ci gaba da biyan alawus na shugabanci (duty post allowance), da kuma share mana hawaye ta hanyar biyan kudaden karin girma (promotion),” in ji Shugaban AoPSHON.

Ya kara da cewa uwar kungiyar AoPSHON ta kasa ma na alfahari da yadda Gwamnatin Gwamna Abba ke aiwatar da manyan ayyuka a bangaren ilimi a jihar Kano.

Malam Abdussalam ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga ‘ya’yan kungiyar da su ci gaba da kare martabar aikinsu. Ya ce hakan zai taimaka wajen cimma burin Gwamnati na bunkasa harkar ilimi a jihar.

“Mu ne masu aiwatar da tsare-tsaren ilimi, don haka wajibi ne mu yi iya bakin kokarinmu wajen sauke wannan nauyi da Gwamnati ta dora mana,” in ji shi

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button