Labarai

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya, Malam Yusuf Kabir, Ya Gode wa Gwamna Bisa Tagomashin Da Yake Yi wa Ma’aikata

Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya, Malam Yusuf Kabir, Ya Gode wa Gwamna Bisa Tagomashin Da Yake Yi wa Ma’aikata

Daga JB Danlami

A yayin bikin ranar Ma’aikata da aka gudanar a yau, 1 ga Mayu, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya, Malam Yusuf Kabir, ya bayyana muhimmancin wannan rana wajen tunawa da irin jajircewa da gwagwarmayar da ma’aikata ke yi domin ci gaban al’umma. Ya ce wannan rana ce da ake amfani da ita wajen girmama ma’aikata da kuma tunatar da al’umma game da rawar da suke takawa a kowanne fanni na rayuwa.

Malam Yusuf Kabir ya yabawa kokarin da Gwamnan jihar ke yi wajen inganta rayuwar ma’aikata, yana mai cewa: “Ina mai mika godiya ta musamman ga Mai Girma Gwamna bisa kulawar da yake nunawa ma’aikata ta fuskar biyan albashi akan lokaci, karin girma ga ma’aikata masu cancanta, da kuma bayar da bashi mara ruwa domin tallafa musu a harkokin rayuwa.”

Ya kara da cewa irin wannan kulawa daga gwamnati yana ƙarfafa gwiwar ma’aikata wajen ci gaba da yin aiki da gaskiya da rikon amana. Bugu da ƙari, ya bayyana cewa Ranar Ma’aikata dama ce ta tunawa da rawar da ƙungiyoyin ma’aikata suka taka wajen samun ’yancin walwala da ingantaccen yanayin aiki.

Daga ƙarshe, Malam Yusuf Kabir ya yi kira ga ma’aikata da su ci gaba da gudanar da aikinsu da kwazo, da kuma goyon bayan duk wani kokari da gwamnati ke yi domin kyautata harkokin ilimi da ci gaban jihar baki ɗaya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button