Kungiyar Shugabannin Kananan makarantun Sakandare (SUPA) ta karrama Shugaban SUBEB da Lambar yabo.
Kungiyar Shugabannin Kananan makarantun Sakandare (SUPA) ta karrama Shugaban SUBEB da Lambar yabo.

Kungiyar Shugabannin Kananan makarantun Sakandare (SUPA) sun karrama Shugaban SUBEB da Lambar yabo.
Daga JB Danlami
Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na jiha, Malam Yusif Kabir ya bukaci kungiyoyin ma’aikata musamman masu nasaba da harkokin hukumar, su ci gaba da wayar da kan ‘ya’yan kungiyoyinsu muhimmanci hada kai da yin biyayya ga dokoki da ka’idojin aiki domin samun nasara a yunkurinsu na samun ci gaba mai ma’ana
Shugaban hukumar ya bayyana bukatar hakan a lokacin da yake karbar lambar yabo daga Kungiyar Shugabannin Kananan makarantun Sakandare reshen jiha a wani taro da ya gudana a dakin taro na SBMC dake sakatariyar Audu Bako.
Malam Yusif ya nanata muhimmanci kungiyoyi wajen lalubo hanyoyin inganta ayyuka da hada kai don magance duk wata matsala da ta shafi aiki, don haka ya hori membobin wannan kungiya da su kaucewa yi duk wani abu da ba ya kan ka’ida.
Da yake godewa kungiyar bisa wannan karramawa Shugaban Hukumar ta Ilimin Bai Daya ya yi alwashin tafiya tare da wannan kungiya a wani mataki na inganta harkokin ilimi.
A jawabinsa tun da fari, shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan makarantun Sakandare reshen Jiha, Malam Abubakar Sule, ya ce kungiyar ta yanke shawarar karrama shugabn Hukumar ne, don nuna godiyarsu bisa yadda yake aiki tukuru, wajen dawo da martabar hukumar ta sauya fasalin ta da dorata kan ingantaccen tsari
Muna godiya da yadda shugaban ya bullo da sabon tsari na zabar shugabanni makarantu wadanda suka cancanta da amincewa a sanya musu kudin masu yin jagoranci har ila yau da samar musu da kayan aiki a makamantansu. In ji Shugaban Kungiyar


