Labarai

Hukumar Ilimin Bai Daya Ta Jiha Ta Horas Da Malamai Kan Jagoranci Da Ba Da Shawarwari Ga Dalibai

Hukumar Ilimin Bai Daya Ta Jiha Ta Horas Da Malamai Kan Jagoranci Da Ba Da Shawarwari Ga Dalibai

Daga

Usman Da’u Isah /JB Danlami

Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jiha ta shirya taron bita na yini biyu domin horas da malamai kan dabarun bayar da jagoranci da ba da shawarwari ga dalibai.

Da yake bude taron bitar a Cibiyar Horar da Malamai da ke Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, da ke babban birnin jiha, Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya na Jiha, Malam Yusuf Kabir ya bayyana cewa, fannin bayar da jagoranci da shawarwari yana da matukar muhimmanci wajen taimaka wa dalibai su fahimci yadda za su gudanar da rayuwarsu da kuma zabin hanyoyin da za su bi domin amfanar da kansu da kuma al’umma gaba daya.

Shugaban hukumar, wanda ya samu wakilcin Daraktar Kula da Harkokin Makarantu, Hajiya Magajiya Usman, ya bayyana cewa fannin bayar da shawarwari yana taimakawa wajen gina kyakkyawar dangantaka tsakanin malamai da dalibai. Haka zalika, yana taimakawa wajen rage matsalolin rayuwa da dalibai ke fuskanta tun da wuri, wanda hakan na iya rage musu damar samun ingantacciyar rayuwa.

Malam Yusuf ya ja hankalin mahalarta taron da su mayar da hankali sosai kan abin da za a koyar da su, yana mai jaddada cewa an zabo su ne bisa cancanta. Saboda haka, ya bukaci su dauki taron da muhimmanci, domin zai taimaka matuka ga ci gaban ilimi a jihar.

Ya kuma yi amfani da damar wajen mika godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa kulawar da yake bai wa hukumar, wanda hakan ke taimakawa wajen bullo da tsare-tsaren da ke bunkasa ilimi a matakin farko.

A nata jawabin, Daraktar Kula da Harkokin Makarantu, Hajiya Magajiya Usman, ta bayyana cewa an zabo malamai da jami’an duba makarantu 200 daga makarantun gwaji, kananan makarantun sakandare da makarantu Islamiyya, da kuma sassan ilimi domin horas da su sabbin dabaru kan bayar da jagoranci da shawarwari.

Wannan, a cewarta, zai taimaka wajen magance matsalolin da dalibai ke fuskanta, wadanda ke hana su yin fice a fannin karatu da sauran al’amuran rayuwa.

Hajiya Magajiya ta kuma gode wa shugaban hukumar bisa yadda yake amfani da gogewarsa wajen bullo da shirye-shiryen da ke inganta harkar ilimi a jihar.

Dr. Yakubu Anas, Babban Jami’in Cibiyar Yusfa kuma mai jagorantar taron bitar, ya bayyana fatan cewa bayan kammala bitar, za a samu sauye-sauye na ci gaba a fannin bayar da jagoranci da shawarwari ga dalibai a fadin jihar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button