Gwagwarmayar takara ba ta raggo ba ce- Hon Rabiu Saleh Gwarzo
Gwagwarmayar takara ba ta raggo ba ce- Hon Rabiu Saleh Gwarzo
Daga
Jb Danlami
Shugaban Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Honarabul Rabiu Saleh Gwarzo, ya yi kira ga tsofaffin ’yan takarar kansiloli na jam’iyyar NNPP wadanda ba su samu damar tsayawa takara a zabukan kananan hukumomi da suka gabata ba, da su dauki wannan lamari a matsayin kaddara tare da hakuri da juriya.
Hon. Rabiu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin wakilan kungiyar tsofaffin ’yan takarar kansiloli daga mazabun Karamar Hukumar Gwarzo, wadanda suka kai masa gaisuwar Sallah a ofishinsa.
A yayin zantawarsa da tawagar, Hon. Rabiu ya bayyana cewa tsayawa takara ba ya nufin dole sai mutum ya yi nasara. Ya jaddada cewa yakamata wadanda ba su samu nasara ba su dauki darasi daga abubuwan da suka fuskanta domin gyara shiri da ƙara daura damara a nan gaba.
” Tsayawa takara ba ta raggo ba ce don haka a siyasance, samun damar tsayawa takara wata nasara ce, amma rashin kai labari bai kamata ya rage maka kwarin gwiwa ba. Dole ne mutum ya koyi darasi daga kowace irin matsala domin ƙarfafa kansa a gaba,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar wa tawagar cewa zai ci gaba da tafiya tare da su domin ƙarfafa musu gwiwa da kuma tallafa musu a kokarin ci gaban yankinsu.Bugu da ƙari, Hon. Rabiu ya yi amfani da damar wajen jinjina ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa irin kokarin da suke yi na kawo ci gaba a jihar, musamman a yankin Gwarzo da kewaye.
A nasa jawabin, jagoran tawagar, Hon. Zakari Isah Muhammad, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ce domin taya shugaban murnar Sallah da kuma neman goyon bayansa ga ƙungiyarsu a ƙoƙarin ci gaba da raya Karamar Hukumar Gwarzo.
Hon. Zakari ya jaddada cewa kodayake ba su samu damar tsayawa takara ba, hakan ba zai zamo hujja ba gare su na kawo cikas ko tsaiko ga jam’iyya ko shugabanninta. Ya ce za su ci gaba da ba da gudummawa wajen ganin an kai Karamar Hukumar Gwarzo Tudun Mun Tsira.
A karshe, ya yaba da irin karimcin da Shugaban Hukumar ya nuna wajen tarbar tawagar, tare da yi masa fatan alheri a ayyukansa na ci gaba.



