Education

KH Makoda raba Littattafan Rubutu 5,000 ga makarantun yankin

KH Makoda raba Littattafan Rubutu 5,000 ga makarantun yankin

Daga JB Danlami

An gudanar da wani muhimmin taro a karamar hukumar Makoda inda aka nuna cikakken goyon baya ga bangaren ilimi ta hanyar rabon kayan karatu ga dalibai.

A wajen taron, Shugaban Karamar Hukumar Makoda, Hon. Auwal Isha Jibga, tare da hadin gwiwar manyan jami’ai da shugabannin gargajiya, sun jagoranci rabon littattafan rubutu guda dubu biyar (5,000) ga makarantun yankin domin inganta koyarwa da koyo.

Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Auwal Isha Jibga, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na bunkasa ilimi a yankin, inda ya bayyana cewa rabon littattafan wani bangare ne na kokarin rage matsalolin karatu da dalibai ke fuskanta. Ya kara da cewa wannan mataki ya yi dai da kudurin Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wadda ta bai wa sha’anin ilimi fifiko na musamman.

Hakazalika, ya bayyana cewa Karamar Hukumar Makoda na daya daga cikin kananan hukumomin da ke cin gajiyar ayyukan raya ilimi da Gwamnatin Jiha ke aiwatarwa, wadanda suka hada da gina sabbin ajujuwa, gyaran tsofaffin dakunan karatu, da kuma horar da malamai domin inganta kwarewarsu.

Haka kuma, Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar, Mujittapha Yunusa Umar Maitsida’u, ya gabatar da jawabin godiya inda ya yabawa wannan shiri tare da bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka matuka wajen saukaka wa malamai da dalibai wajen gudanar da harkokin koyo da koyarwa yadda ya kamata

Hon. Auwal Isha Jibga ya kuma yi alkawarin cewa shi da mataimakinsa, tare da hadin gwiwar zababbun kansiloli da naddadu, za su rika buga tare da rabon karin littattafan rubutu guda dubu daya (1,000) a duk wata. Wannan shiri zai ci gaba har sai an rufe dukkan mazabu goma sha daya (11) da ke karamar hukumar Makoda.

Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar, Mujittapha Yunusa Umar Maitsida’u, ya gabatar da jawabin godiya inda ya yabawa wannan shiri tare da bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka matuka wajen saukaka wa malamai da dalibai wajen gudanar da harkokin koyo da koyarwa yadda ya kamata.

Masana ilimi sun dade suna jaddada muhimmancin samar da wadatattun kayan koyo da koyarwa a makarantu, kasancewar hakan na taimakawa wajen kara fahimtar darussa, inganta sakamakon dalibai, da kuma rage yawan ficewar yara daga makaranta. Samun littattafan rubutu ga dalibai na kuma kara musu kwarin gwiwa da sha’awar karatu, tare da bai wa malamai damar gudanar da darussa cikin tsari mai kyau.

Al’ummar yankin sun yabawa wannan yunkuri, inda suka bayyana cewa zai taimaka matuka wajen inganta ilimi da kuma kara kwarin gwiwar dalibai a makarantun firamare da sakandare.

Wakilinmu na yankin Lawan Mati Makoda ya rawaito mana cew Wannan mataki na nuna irin muhimmancin da shugabannin yankin ke bai wa ilimi a matsayin ginshikin ci gaba da makomar al’umma.

Related Articles

Back to top button